Luke 3

Yohanna Mai Baftisma Ya Shirya Hanya

1A shekara ta goma sha biyar ta mulkin Kaisar Tiberiyus, lokacin kuwa Buntus Bilatus ne gwamnar Yahudiya, Hiridus kuma yana sarautar Galili, ɗanʼuwansa Filibus yana sarautar Ituriya da Tarakunitis, Lisaniyas kuwa yana sarautar Abiline—  2a lokacin da Annas da Kayifas suke manyan firistoci, sai maganar Allah ta zo wurin Yohanna, ɗan Zakariya a hamada. 3Ya zaga dukan ƙasar da take kewaye da Urdun, yana waʼazin baftismar tuba don gafarar zunubai. 4Kamar yadda yake a rubuce a littafin annabi Ishaya:

“Muryar mai kira a hamada,
‘Ku shirya wa Ubangiji hanya,
ku miƙe hanyoyi dominsa.
5Za a cike kowane kwari,
a farfashe kowane dutse da kowane tudu.
Za a miƙe hanyoyin da suka karkace,
a gyaggyara hanyoyi masu gargaɗa su zama sumul.
6Dukan ʼyan Adam kuwa za su ga ceton Allah!’ ”
Ish 40.3-5


7Yohanna ya ce wa taron da suke zuwa domin yǎ yi musu baftisma, “Ku macizai! Wa ya gargaɗe ku, ku guje wa fushin nan mai zuwa? 8Ku yi ayyukan da suka dace da tuba. Kada ma ku yi tunani za ku iya ce wa kanku, ‘Ai, muna da mahaifinmu Ibrahim.’ Ina gaya muku cewa daga cikin duwatsun nan Allah zai iya ta da ʼyaʼya wa Ibrahim. 9An riga an sa bakin gatari a gindin itatuwa, kuma duk itacen da bai ba da ʼyaʼya masu kyau ba, za a sare shi a jefa cikin wuta.”

10Sai taron suka tambaye shi, suka ce “To, me za mu yi ke nan?”

11Ya amma ya ce, “Ya kamata, mutumin da yake da riguna biyu, yǎ raba da wanda ba shi da riga, mai abinci kuma yǎ yi haka.”

12Masu karɓar haraji ma suka zo, domin a yi musu baftisma. Suka yi tambaya, suka ce “Malam, me ya kamata mu yi?”

13Ya ce musu, ya ce, “Kada ku karɓa fiye da abin da aka ce a karɓa.”

14Sai waɗansu sojoji suka tambaye shi, “Mu fa? Me ya kamata mu yi?” Sai ya amsa, ya ce, “Kada ku ƙwace kuɗin mutane, kada kuma ku yi shaidar ƙarya. Ku yi haƙuri da abin da ake biyanku.”

15Mutane suka zuba ido, suna kuma tunani a zuciyarsu, ko Yohanna ne Kiristi wanda ake sauraron zuwansa. 16Yohanna ya amsa musu duka, ya ce, “Ina muku baftisma da ruwa. Amma wani wanda ya fi ni iko yana zuwa, ban ma isa in kunce igiyar takalmansa ba. Shi zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki da wuta kuma. 17Matankaɗinsa yana a hannunsa don yǎ tankaɗe sussukarsa ya kuma tattara alkama cikin rumbunsa, amma zai ƙone yayin da wutar da ba a iya kashewa.” 18Da kalmomi masu yawa Yohanna ya yi wa mutane gargaɗi, ya kuma yi musu waʼazin bishara.

19Amma da Yohanna ya tsauta wa Hiridus mai mulki saboda Hiridiyas, matar ɗanʼuwansa, da kuma dukan sauran mugayen abubuwan da ya yi, 20Hiridus dai ya ƙara ɓata alʼamarin: Ya sa a kulle Yohanna a kurkuku.

Baftismar Yesu da kuma Asalinsa

21Saʼad da ake wa dukan mutane baftisma, sai aka yi wa Yesu shi ma. Da yana cikin adduʼa, sai sama ya buɗe, 22Ruhu Mai Tsarki kuma ya sauko masa a wata siffa, kamar kurciya. Sai murya ta fito daga sama, ta ce, “Kai ne Ɗana, wanda nake ƙauna, kai ne kuma kana faranta mini zuciya ƙwarai.”

23To, Yesu kansa yana da shekaru kusan talatin da haihuwa saʼad da ya fara aikinsa. An ɗauka shi ɗan Yusuf ne,

ɗan Heli,
24ɗan Mattat,
ɗan Lawi, ɗan Melki,
ɗan Yannai, ɗan Yusuf,
25ɗan Mattatiyas, ɗan Amos,
ɗan Nahum, ɗan Esli, ɗan Naggai,
26ɗan Maʼat,
ɗan Matatiyas, ɗan Semeyin,
ɗan Yosek, ɗan Yoda,
27ɗan Yowanan, ɗan Resa,
ɗan Zerubbabel, ɗan Sheyaltiyel,
ɗan Neri,
28ɗan Melki,
ɗan Addi, ɗan Kosam,
ɗan Elmadam, ɗan Er,
29ɗan Yoshuwa, ɗan Eliyezer,
ɗan Yorim, ɗan Mattat,
ɗan Lawi,
30ɗan Simeyon,
ɗan Yahuda, ɗan Yusuf,
ɗan Yonam, ɗan Eliyakim,
31ɗan Meleya, ɗan Menna,
ɗan Mattata, ɗan Natan,
ɗan Dawuda.
32ɗan Yesse,
ɗan Obed, ɗan Bowaz,
ɗan Salmon,
Waɗansu rubuce rubucen hannu na farko farko suna da Sala
ɗan Nashon,
33ɗan Amminadab, ɗan Ram,
Waɗansu rubuce rubucen hannu suna Amminadab, ɗan Admin, ɗan Arni; waɗansu rubuce rubucen hannun kuma sun bambanta sosai.

ɗan Hezron, ɗan Ferez,
ɗan Yahuda,
34ɗan Yaƙub,
ɗan Ishaku, ɗan Ibrahim,
ɗan Tera, ɗan Nahor,
35ɗan Serug, ɗan Reyu,
ɗan Feleg, ɗan Eber,
ɗan Shela.
36ɗan Kainan,
ɗan Arfazad, ɗan Shem,
ɗan Nuhu, ɗan Lamek,
37ɗan Metusela, ɗan Enok,
ɗan Yared, ɗan Mahalalel,
ɗan Kenan,
38ɗan Enosh,
ɗan Shitu, ɗan Adamu,
ɗan Allah.
Copyright information for HauSRK